Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Mammabobin tawagar ruwan Sumood da ke kan hanyar zuwa Gaza sun sanar da cewa sun kasance a tazarar kilomita 322 zuwa Gaza. Wannan wajen da suka kai kuwa shine wajen da a baya sojojin Isra'ila suka dakatar da jiragen ruwan Madeleine da Hanzala.
A wannan karon tawagar Sumood na kasa da kasa suna kan hanyarsu ta zuwa Gaza dauke da jiragen ruwa kimanin 50 da masu fafutuka sama da 500, tare da taimakon agaji, kuma idan Isra'ila ba ta hana su ba, za su isa gabar tekun da aka yi wa kawanya nan da kasa da kwanaki uku.
Your Comment